Firaministan kasar Sin ya jaddada alamun samun karko da cigaban tattalin arziki mai inganci
Firaministan kasar Sin Li Keqiang a ranar talatan nan 4 ga wata ya jaddada cewar dole ne kasar ta zurfafa kwaskwarimar data ke yi domin cigaba da samun karko da cigaban tattalin arziki ingantacce a yanzu da take fuskantar wani yanayi mai sarkakkiya a fannin tattalin arziki.
Mr Li ya furta hakan ne lokacin da yake halartan wani tattaunawa da masu bada shawarar siyasa daga bangarorin tattalin arziki da aikin noma a cigaba da zaman taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC karo na 12 wanda shine matakin koli na shawarwarin siyasa a kasar. (Fatimah Jibril)