in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin
2014-03-03 16:14:49 cri

A yau ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 12 da yamma a zauren babban dakin taruwar jama'ar kasar ne Sin da ke a nan birnin Beijing. Shugabannin kasar Sin ciki har da Xi Jinping, da Li Keqiang da dai sauransu sun halarci taron.

Da farko sai da dukkan mahalartan taron sun nuna jimami ga mutanen da suka rasa rayuka a mummunan harin ta'addancin da aka kai a tashar jiragen kasa ta birnin Kunming na lardin Yunnan a ran 1 ga wata da dare. Sa'an nan kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mista Yu Zhengsheng ya gabatar da rahoton aiki da zaunannen kwamitin ya shirya, inda ya waiwaiyi da takaita aikin da sabuwar majalisar take gudanarwa, tare da shirya ayyukan da za ta yi a shekarar 2014.

Za a rufe taron ne a ranar 12 ga wata da safe. Wakilan majalisar fiye da dubu 2 da 100 ne za su ba da shawarwarinsu kan manyan batutuwa a fannoni daban daban ciki har da siyasa, da tattalin arziki da zaman al'umma da dai sauransu.

A yayin da ya ke gabatar da rahoton aikin zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a taron na yau, Mr Yu Zhengsheng ya ce, shekara ta 2013, ita ce shekarar da aka aiwatar da manufofin jagorancin taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da kuma yadda taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya tafiyar tare da inganta hanyoyin sa.

Ya ce an cimma nasarori a yayin da ake aiwatar da gyare-gyare,inganta tsarin demokiradiya ta hanyar yin shawarwari da tuntubar juna da kuma inganta tsarin aiki.(Danladi,Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China