Kasar Sin ta yi juyayin mutuwar wadansu mutane sakamakon cin karon da wata motar jif ya yi da gadar Jinshui a Beijing
Ranar 30 ga wata, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, sakamakon wata motar jif da ta ci karo da gadar Jinshui da ke dab da babban filin Tian'anmen da ke nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda wasu mutane suka jikkata ko mutu, ciki had da 'yan kasashen waje 5. Kasar Sin ta yi bakin ciki kan lamarin, tare da nuna juyayin mutuwar wadanda ba su aikata wannan laifi ba, tare da jajanta ma iyalansu da kuma wadanda suka ji rauni.
Madam Hua ta kara da cewa, bayan abkuwar lamarin, hukumomin kasar Sin sun dauki matakai nan take ba tare da bata lokaci ba domin bai wa wadanda suka jikkata jinya cikin lokaci kuma yadda ya kamata. Kana kuma bangaren Sin ya sanar wa ofisoshin jakadancin kasashen waje da abin ya shafa da ke nan kasar Sin lamarin, ya kuma bai wa jami'an jakadanci na wadannan kasashe sauki wajen ziyartar wadanda suka jikkata da kuma gudanar da ayyukansu. Kakakin ta ba da tabbacin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimakon da ya wajaba wajen daidaita harkokin da abin ya shafa. (Tasallah)