in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai harin ta'addanci a gundumar Shanshan da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin
2013-06-28 15:55:56 cri
Ran 26 ga wata da sassafe misalin karfe 5 da minti 50, an kai farmaki a garin Lukeqin da ke gundumar Shanshan na yankin Turpan da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda 'yan ta'adda suka kai hari a caji-ofis, rundunar 'yan sanda masu sintiri, gwamnatin garin da kuma wuri aikin kwadago, har suka kone motocin 'yan sanda.

Mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon harin, ciki hadda 'yan kabilar Uygur guda 16, da kuma 'yan sanda guda 2, kana mutane 21 sun jikkata.

Masu aikin tsaro sun harbe 'yan ta'adda guda 11 yayin harin, sannan sun cafke guda 4.

A halin yanzu dai, an samu kwanciyar hankali a wurin bisa kokarin masu aikin tsaron. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China