Wakilin zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, Yu Zhengsheng ne ya yi wannan tsokaci, yayin da yake jawabi ga mahalarta taron wayar da kai kan yaki da ayyukan ta'addanci da ya gudana a Urumqi, babban birnin Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, da marecan ranar Asabar 29 ga wata.
Yu ya ce mahukuntan kasar Sin za su ci gaba da hukunta wadanda ke da burin ta da zaune tsaye, tare da daukar dukkanin matakan da suka dace wajen dakile ayyukan 'yan ta'adda, da na masu tsattsauran ra'ayi. Daga nan sai wakilin ya yi kira ga jama'ar yankin da su kwantar da hankulansu, su kuma lura da dukkanin wani bakon yanayi da ba su amince da shi ba.
Shi ma a nasa jawabi memban hukumar siyasa na babban kwamitin jam'iyyar kwaminis ta jama'ar kasar Sin Meng Jianzhu, cewa ya yi akwai bukatar jami'an 'yan sanda masu dauke da makamai, su ci gaba da gudanar da sintiri a ko da yaushe a yankin, domin kare rayukan al'umma da kabilun dake jihar baki daya. A cewarsa wannan jiha ta Xinjiang na ci gaba da samun habaka ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa, sai dai 'yan ta'adda, da masu tsattsauran ra'ayi, da kuma 'yan taware, na ci gaba da daukar matakan ta da hargitsi da fitina a yankin, a yunkurin da suke yi na mai da hannun agogo baya. Meng ya ce hare-haren baya-bayan nan da suka auku a jihar sun haddasa rasa rayuka da barnata dukiyoyi da dama, tare da dagula kyakkyawan yanayin zamantakewar al'ummar yankin, don haka ya sake kira ga 'yan sanda masu dauke da makamai, da su tabbatar sun zartas da kudurorin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda ya tanaji daukar matakan dakile ayyukan bata-gari. (Saminu Alhassan)