A cikin sanarwar, an ce, an kai harin ta'addanci da gangan a wuraren zirga-zirga da ke cike da mutane, kwamitin sulhu na M.D.D. ya yi mamaki game da harin, tare da yin Allah-wadai da lamarin da kakkausar harshen.
A sa'i daya kuma, kwamitin sulhu na M.D.D. ya sake jaddada cewa, za a yaki da ta'addanci ta ko wace hanya bisa tsarin kundin mulki na M.D.D..
A wannan rana kuma, babban magatakardar M.D.D. Ban Ki-moon ya buga waya ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, inda ya nuna jejeto ga dangogin mutanen da suka rasu cikin harin tare da al'ummar Rasha.(Bako)