in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kai hari ofishin jakadancin Rasha dake Syria
2013-11-29 10:54:52 cri
Ran 28 ga wata, rundunar sojan gwamnatin kasar Syria ta sanar da mamaye garin Dayr Atiah dake arewacin wajen birnin Damascus, koda yake ya zuwa yanzu an dawo da yanayin zaman lafiya da karko a garin dake da muhimmanci ga tsarin sojan kasar.

Haka zalika bisa labaran da aka samu daga kamfanonin dillacin labaran wurin, an ce, an samu wata fashewa a dandalin ofishin jakadancin kasar Rasha dake kasar ta Syria wadda ta yi wa ginin ofishin barna. A wannan rana da dare, wani jami'in kula da harkokin labarai na kasar Rasha dake kasar Syrian ya gaskata cewa, harin ya haddasa mutuwar wani dan Syria, yayin da wasu 'yan Syria masu kula da harkokin tsaro suka jikkata.

Kafin wannan, da ma dakarun 'yan adawa na kasar ta Syria sun sha kai hare-hare da bindigogi masu lugudan wuta kan ofishin jakadancin kasar ta Rasha dake Syria.a yanzu haka, gwamnatin kasar Syria ta riga ta karfafa matakan tsaro a yankunan dake kewayen ofishin jakadancin kasar ta Rasha dake kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China