in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Putin ya ba da umurnin kara yaki da ta'addanci a kasar Rasha
2013-12-31 11:24:44 cri
Game da hare-haren ta'addanci da aka kai guda 2 a jihar Volgagrad dake kasar Rasha, a jiya litinin 30 ga wata, shugaban kasar Vladimir Putin ya gana da firaministan kasar Dmitri Medvedev da ministan kula da harkokin cikin gida na kasar Vladimir Kolokoltsev da shugaban hukumar tsaro ta tarayyar Rasha Aleksandr Bortnikov, inda ya ba da umurni ga hukumar yaki da ta'addanci da ta tabbatar da tsaro a kasar, da kara daukar matakan tsaro a jihar Volgagrad.

Shugaban Putin ya bukaci hukumar yaki da ta'addanci da ta mika rahoton yanayin tsaro da na matakan tsaro da ta dauka a kasar gare shi a kullum, a sa'i daya kuma, a inganta matakan tsaro a kasar. A nasa bangaren, shugaban hukumar tsaro ta tarayyar Rasha Bortnikov ya mika rahoton yaki da ta'addanci da hukumar tsaro da sauran hukumomin leken asirin suka samu ga shugaban Putin.

Haka kuma, bayan da ministan kula da harkokin cikin gida Kolokoltsev ya yi shawarwari da Putin, aka ba shi aikin zuwa jihar Volgagrad, kuma bisa abubuwan da ke kunshe cikin rahoton da ya mika wa Putin, an ce, a wannan rana, ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kara daukar matakan yaki da ta'addanci, kuma kwanan baya, sojojin hukumar tsaro da ma'aikatar kula da harkokin cikin gida sun murkushe hare-haren ta'addanci da aka yi shrin kai wa yankunan Dagestan da Stavropol a dutsen Caucasia.

A ranar 29 da ranar 30 ga wata, cikin dan lokaci, aka kai hare-haren ta'addanci guda 2 ga birnin Volgagrad dake yankin kudancin kasar, abin da yayi sanadiyar mutuwar mutanen sama da 30, tare da jikkatar wasu kimanin kusan 70.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China