Wang Yi ya ce, bisa goron gayyatar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da za a yi a birnin Sochi, abin da ya nuna irin goyon bayan juna da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha. Ya yi imani cewa, ziyarar shugaba Xi a birnin Sochi za ta samu cikakkiyar nasara, kuma zai nuna dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha, tare da bude wani sabon babi na raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a cikin shekarar 2014.
Lavrov a nasa bangaren ya ce, Rasha tana zuba ido game da halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta Sochi da shugaba Xi Jinping zai yi, kuma tana fatan hada gwiwa da kasar Sin, don tabbatar da ziyarar shugaba Xi a Rasha lami lafiya.(Bako)