in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Amurka da Rasha sun tattauna game da taron kasa da kasa kan batun Siriya
2014-01-22 16:36:00 cri
A ranar 21 ga wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya buga waya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda bangarorin biyu suka tattauna game da taron kasa da kasa kan batun Siriya da za a fara a yau.

Fadar White House ta Amurka ta ba da wata sanarwa cewa, shugabannin kasashen biyu sun tattauna halin da ake ciki a kasar Siriya, ciki har da yadda ake share fagen shirya taron kasa da kasa kan kasar Siriya, da jigilar makamai masu guba daga kasar Siriya da lalata su. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da hadin gwiwa a kan batun nukiliya na kasar Iran, da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da za a yi a Sochi. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China