in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya gamsu da dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin
2014-01-20 12:13:53 cri

A ranar 19 ga wata, bisa labarin da tashar Internet ta fadar shugaban kasar Rasha ta bayar, an ce, kwanan baya, yayin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ke zantawa tare da manema labaru a birnin Sochi dake yankin kudancin kasar. Ya ce, an kara yaukaka dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen Rasha da Sin bisa manyan tsare-tsare, kuma Rasha ta nuna gamsuwarta kan irin wannan dangantaka.

A ranar 17 ga wata, a gabannin bude taron gasar wasannin Olympics da za a yi a birnin Sochi a lokacin sanyi, Putin ya yi hira da manema labaru na gida da waje da dama, ciki har da gidan telebijin kasar Sin CCTV. Yayin da Putin ke zantawa da dan jarida na kasar Sin, ya ce, kasashen Rasha da Sin sun inganta hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu da harkokin tsaro. Yana ma fatan hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a kan iyakokinsu za ta kara inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Game da tababar da wasu kasashe da kungiyoyi da suke kan sakamakon da aka samu tun bayan yakin duniya na biyu, Putin ya ce, ba za a iyar sauya wannan sakamakon da aka samu ba, domin an tabbatar da shi bisa wasu dokokin kasa da kasa, kullum kasar Rasha tana nacewa ga aiwatar da daidaiton da aka cimma bisa yarjejeniyar kasa da kasa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China