Shugaba Zuma a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, ana gudanar da zaben bayan duk shekaru biyar ba tare da fashi ba sannan wannan zaben da za'a yi zai zama na tarihi saboda lokacin za'a cika shekaru 20 da samun 'yanci daga kangin wariyar launin fata.
Mr. Zuma ya ce, wa'adin wannan gwamnatin mai ci yanzu zai kare a ranar 22 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki.(Fatimah)