Yajin aiki da bangarorin hakar zinari da karfen Platine da kungiyar ma'aikatan ma'adinai da kungiyoyin kamfanonin gine-gine na (AMCU) suka dauki shiga, an jinkirtar da shi har wani lokaci, in ji kwamitin sasantawa da shiga tsakani na kasar Afrika ta Kudu (CCMA) a ranar Laraba.
Sanarwar ta biyo bayan da wata kotun aiki ta kasar ta yanke hukuncin cewa, AMCU ba ta da hurumin shiga yajin aiki tare da ma'aikatan ma'adinan zinari har zuwa ranar 30 ga watan Janairu.
Mun yi imanin cimma wata mafita ta hanyar shawarwari da za ta taimakawa bangarorin biyu da ma Afrika ta Kudu baki daya, kuma a shirye muke mu kawo taimakonmu domin cimma wannan mafita, in ji kwamitin CCMA.
Cibiyar dake kula da harkokin ma'adinai ta kai kara kotun Johannesburg, domin samun wani matakin da zai hana mambobin AMCU shiga yajin aiki.
Kungiyar 'yan kwadagon ta shirya shiga yajin aikin gama gari a bangaren hakar zinari da na karfen Platine, a ranar Alhamis bayan ta sanar da magoya bayanta ta wannan yakin aiki.
Kungiyar na bukatar karin albashin a kowane wata na kudin Rands 12500 kwatankwacin dalar Amurka 1200 ga sabbin ma'aikata.
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma da kuma jam'iyyar ANC suna fatan ganin an warware wannan matsala kafin zabubukan kasar na watan Afrilu. (Maman Ada)