in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu ya gana da mataimakin shugaba na Sin
2013-12-12 09:56:06 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao da ya halarci bukukuwan jana'izar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela a matsayin wakilin musammun na shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Laraba a birnin Pretoria.

Mista Li ya mika wa Jacob Zuma wasikar shugaba Xi Jinping dake bayyana ta'aziyarsa ga shugaban Afrika ta Kudu da sunan gwamnatin Sin da jama'ar kasar baki daya game da mutuwar Nelson Mandela da yake dauka wani babban aminin jama'ar kasar Sin.

A cikin wannan wasika, shugaban kasar Sin ya nuna imanin cewa, al'ummar Afrika ta Kudu za su cigaba da bin tunanin Mandela tare da kara azama wajen kawo sabbin hanyoyin da za su taimakawa cigaban tattalin arziki da na jama'ar kasar, tare da bayyana cewa, kasar Sin a shirye take a ko da yaushe wajen aiki tare da kasar Afrika ta Kudu domin kara zurfafa muhimmiyar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.

Mista Jacob Zuma ya nuna godiyarsa ga shugaba Xi, gwamnati da kuma jama'ar kasar Sin game da jajantawarsu, tare da bayyana cewa, Afrika ta Kudu za ta cigaba da karfafa abokantakar dake tsakanin Afrika ta Kudu da kasar Sin da Mandela ya shimfida.

Gwamnatin Sin da jama'ar kasar na alfahari sosai da huldar dake tsakanin Sin da Afrika ta Kudu, kuma za su yi aiki tare Afrika ta Kudu wajen kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin shugabannin kasashen biyu domin kara zurafafa dangantakarsu daga dukkan fannoni. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China