Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta yi kira da a fadada hadin gwiwa mai kyau tare da Najeriya, kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afrika a bangaren harkokin yawon bude ido da zuba jari.
Mista Thulani Nzima, shugaban gudanarwa na ma'aikatar yawon bude ido ta kasar Afrika da Kudu (SATB) ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, dalilin haka shi ne domin karfafa dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Kuma hakan zai samar da wani tsarin aiki na tatttaunawa batutuwan da za su iyar bullowa a harkokin yawan shakatawa da na bunkasa zuba jari, in ji mista Nzima.
Haka kuma jami'in ya jaddada cewa, dangantaka mai karfi tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu a fannin zuba jari da yawon shakatawa zai kara janyo karin alfanun kasuwanci ga banagrori da kwararru a fannin yawon bude ido a cikin kasashen biyu.
A cewarsa, ma'aikatar yawon bude ido ta dauki niyyar kara ba da muhimmanci ga tunanin yawon bude ido irin na kare muhalli, tare da bayyana cewa, ma'aikatarsa za ta shirya bikin baje kolin harkokin yawon bude ido da na kasuwanci na kwanaki uku a shekara mai zuwa, wanda zai hada masu saye da sayarwa, masu shirya baje koli, kwararru a fannin yawon bude ido, ganin za a bunkasa harkokin yadda ya kamata. (Maman Ada)