in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fim din tarihin rayuwar Mandela na samun karbuwa a Afirka ta Kudu
2013-11-29 10:15:46 cri

Rahotanni daga Afirka ta Kudu na cewa, sabon fim din nan da aka shirya, mai kunshe da tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela, na samun karbuwa a dukkanin fadin kasar.

Fim din wanda aka shirya bisa jigon littafin tarihin rayuwar tsahon dan gwagwarmayar mai suna "Long Walk to Freedom", aka kuma fara nunawa a gidajen sinimar kasar a ranar Alhamis, ya samu 'yan kallo masu tarin yawa daga dukkanin sassan al'ummun kasar.

Tuni dai aka kaddamar da wannan fim a ranar 10 ga watan Satumabar da ya gabata a birnin Toronto, yayin bikin baje kolin fina-finan da aka gudanar a wannan lokaci.

Fim din na sa'o'i biyu, a cewar mashiryinsa Anata Singh, an shafe shekaru 25 ana shirya shi, ya kuma yi fatan zai samu cikakkiyar karbuwar da ta dace da ma'anarsa. Har ila yau, ana fatan fidda shi kasashen Faransa da Amurka cikin wata mai zuwa.

Mandela wanda a yanzu haka ke da shekaru 95 a duniya, shi ne zababben shugaban kasar Afirka ta Kudu na farko, ya kuma sha gwagwarmaya da yaki da akidar nuna banbancin launin fata, kafin zabensa a shekara ta 1994. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China