Ofishin lura da dangantakar kasashen waje a Afirka ta Kudu DIRC, ya bayyana gamsuwa da yarjejeniyar da kasashen nan 6 suka cimma da Iran, don gane da batun nukiliyar kasar.
A ta bakin kakakin ofishin na DIRC Clayson Monyela, Afirka ta Kudu na yabawa dukkanin wani yunkuri na warware wannan batu cikin ruwan sanyi. Monyela ya kara da cewa, kwarya-kwaryar 'yarjejeniyar da sassan biyu suka rattabawa hannu a ranar 24 ga wannan wata na Nuwamba, na da matukar tasiri ga batun nukiliyar Iran. Daga nan sai ya yi fatan cewa, za a baiwa Iran din damar sarrafa makamashin Uranium bisa dokar da ta tanajin yin hakan a sassan da ba na kirar makamai ba.
Har ila yau, jami'in ofishin na DIRC ya bukaci kasashen duniya, da su baiwa hukumar makamashin nukiliya ta duniya, ko IAEA cikakkiyar damar aiwatar da ayyukanta a kasar ta Iran bisa doron doka.
A makon da ya shude ne dai Iran ta amince da wani kuduri, mai zangon watanni 6, da ya tanaji rage yawan ayyukanta, masu alaka da sarrafa sinadarin Uranium, bisa sharadin dage takunkumin da ya hana ma ta samun tallafin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 7. (Saminu)