in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai a Kenya.
2013-12-13 09:50:50 cri

Jiya Alhamis 12 ga watan nan ne aka yi bikin murnar cika shekaru 50 da samun 'yancin kan kasar Kenya.

Bikin wanda ya gudana a babban birnin kasar wato Nairobi, ya samu halartar shugabanni sama da 20, daga kasashen nahiyoyin Asiya da Afirka.

Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wan E'xiang wanda ya zauna a jerin gaba a dakalin shugabanci a matsayin manzon musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin.

Yayin bikin shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya yi kira ga daukacin jama'ar kasar dake da bambanci na kabilu, da addini da su hada kai waje guda, domin cimma burin ci gaban kasa, tare da dukufa wajen gina kasar ta Kenya, don ta kasance mai samun bunkasuwa a fannin tattalin arziki.

A ranar 12 ga watan Disambar shekarar 1963 ne, kasar ta Kenya dake gabashin nahiyar Afirka ta samu 'yancin kai daga turawan Birtaniya, bisa kokarin da jama'ar ta masu yaki da mulkin mallaka suka yi. A kuma ranar 14 ga watan Disambar 1963, kasar ta kafa dangantakar diflomasiyya tare da kasar Sin. Haka zalika, a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 1964, kasar ta zamo jamhuriya mai cikakken ikon mulkin kai wato an kafa kasar Jamhuriyar Kenya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China