Li Keqiang, firaministan kasar Sin, da Yu Zhengsheng, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin sayasa ta kasar Sin, sun gana da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, dake ziyara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a ranar 20 ga wata.
Yayin ganawarsu, fitaminista Li Keqiang na kasar Sin ya ce, Sin na son kara hada kai tare da Kenya don kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2. Sin, a cewar Mista Li, na nuna goyon baya ga kokarin kasashen Afirka na neman dinkuwarsu waje guda, da yunkurinsu na daidaita matsalolin nahiyar da kansu, kana kasar na son tallafawa nahiyar Afirka wajen neman samun zaman lafiya da ci gaba.
A nasa bangaren, Mista Kenyatta ya ce, kasarsa tana ma kasar Sin godiya kan irin taimakon da ta baiwa kasarsa a shekarun da suka gabata, kana tana son koyon fasahar kasar Sin a fannin raya kasa.(Bello Wang)