Bayanan mahalarta taron sun karkata ga kira ga kafofin yada labarun kasar Sin da na kasashen Afrika, da su inganta hadin gwiwa tsakaninsu, domin ganin kasashen Afirka sun kara saninsu kan kasar Sin, kuma kasashen duniya sun kara saninsu kan kasashen Afirka.
A jawabinsa yayin wannan taro, jakadan kasar Sin da ke kasar ta Kenya Liu Guangyuan ya bayyana cewa, yanzu kafofin yada labaru na kasar Sin, sun kafa sassansu a nahiyar Afrika, don kara bayyana wa kasashen duniya ainihin halin da ake ciki a kasashen Afrika, ta hanyar gabatar da shirye-shirye, da ke shafar kasashen na Afrika bisa idon Sinawa. Daga nan sai ya yi kira ga kafofin yada labarun kasar Sin, da na kasashen Afrika da su kara kokartawa, wajen yin mu'amala kai tsaye, da kara fahimtar juna tsakanin jama'ar kasar ta Sin da na kasashen Afrika.
Da yake tsokaci don gane da wannan batu, diraktan cibiyar nazarin yada labaru ta jami'ar Tsinghua Li Xiguang ya bayyana cewa, kamata ya yi kafofin yada labaru na kasar Sin su gabatar da labaru bisa mahangarsu, domin su sha bamban da kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya.
Shi kuwa direktan gudanarwa na cibiyar nazarin demokuradiyya da shugabanci ta kasar Kenya Dennis Khedehou, cewa ya yi, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar kasashen Afrika, amma al'ummar kasashen Afrika da dama ba su fahimci hakikanin alfanun da kasar Sin ke samarwa ba. Ya ce, dole ne kafofin yada labaru na kasar Sin, da kasashen Afrika su inganta hadin gwiwa, don kara bayyana wa jama'ar kasashen Afrika cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya haifar da moriya mai yawa ga kasashen na Afrika.(Bako)