Domin tunawa da ranar cika shekaru 70 da kafa gidan rediyon kasar Sin wato CRI da kuma fara watsa labaru zuwa kasashen waje, CRI ya yi bikin tunawa da asalinsa a ran 25 ga wata a kauyen Shahe na gundumar Shexian ta lardin Hebei na kasar Sin, inda aka yaye kyallen dake alamanta bude tsohon dakin da aka fara gabatar da shirye-shiryen harshen Turanci na rediyon kasar Sin.
A ran 11 ga watan Satumba na shekarar 1947, gidan rediyon Xinhua dake arewacin lardin Shanxi ya fara watsa labaru ga kasashen waje ta harshen Turanci a kauyen Shahe na gundumar Shexian ta lardin Hebei, daga nan, sashen Turanci na CRI ya kafu.
A gun bikin, mataimakin shugaban CRI Xia Jixuan ya ce, sashen Turanci na CRI ya shaida kafuwa da kuma bunkasuwar sabuwar kasar Sin, ya ba da babbar gundummawa ga fadakar da mutanen kasashen waje kan kasar Sin da sada zumunci a tsakanin jama'ar kasar Sin da sauran kasashen duniya.
Ya kuma kara da cewa, a nan gaba, CRI zai ci gaba da kara karfin watsa labaru da kafa tsarin watsa labaru na zamani domin raya aikin watsa labaru ga kasashen waje.
Shugabannin CRI Xia Jixuan da Wang Minghua da Wang Wenjun da shugaban hukumar watsa labaru ta lardin Hebei Xia Wenyi da jami'an gwamnati da kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin na birnin Handan Hui Jian da Jia Yongqing da Hou Huamei da kuma mutane fiye da 100 na cikin gida da na waje sun halarci bikin.(Lami)