Yau Laraba 15 ga wata, tawagar dandalin tattaunawa karo na farko kan raya talibijin na zamani na Afrika ta kai ziyara a gidan rediyon kasar Sin CRI. Mambobin tawagar sun saurari bayanan da aka yi game da CRI, kuma sun yi musayar ra'ayi da mataimakin babban edita Ma Bohui kan wasu batutuwan da suke sha'awa tare da kai ziyara a wasu sassa.
Shugaban tawagar ya bayyana cewa, shekarun nan baya, sha'anin watsa labaru na nahiyar Afrika ya sami bunkasuwa sosai, ba za su manta da taimakon da kasar Sin ta ba su ba. Yanzu, Sin tana taimawaka wasu kasashen Afrika wajen samar da fasaha na zamani cikin sha'anin rediyo da talibijin, abin da ya kawo alheri ga kasashen Afrika fiye da 10. Shirye-shiryen da CRI ke gabatar a nahiyar Afrika sun samar da zarafi mai kyau ga jama'ar Afrika wajen fahimtar kasar Sin.
Ma Bohui ya yi wa tawagar bayanai kan tarihi da bunkasuwar CRI. Ya nuna cewa, CRI tana mai da hankali sosai kan nahiyar Afrika, tana da sassan da dama dake amfani da harsunan Afrika. CRI tana fatan kara hadin kai da kafofin watsa labaru na kasashen Afrika.(Amina)