A ran 15 ga wata a nan birnin Beijing, an yi bikin nuna zane-zane domin murnar cika shekaru 70 da kafa gidan rediyon kasar Sin (CRI), idan daga inda aka nuna nasarorin da kafar watsa labaru ta CRI ta samu a cikin shekaru 70 da suka gabata.
A wani mataki na nuna muhimmin aiki da kafar watsa labaru ke yi na taya ta murnar cika shekaru 70 da kafata, inda akayi bikin nuna zane-zane 120 ko fiye a gun wannan nuni, ciki har da zane-zanen musamman da wasu shahararrun masu zane-zane suka bai wa gidan rediyon kasar Sin domin taya murnar cika shekaru 70 da kafata. Za a cigaba da wannan nuni har zuwa karshen wannan shekara.
Shugaban gidan rediyon kasar Sin Wang Gengnian da shahararre kuma kwararre a fannin fasahar rubutu Ouyang Zhongshi da mataimakin shugaban kungiyar kwararru a fannin fasahar rubutu na kasar Sin Wang Jiaxin da babban jami'in kungiyar masu zane-zane na kasar Sin Huang Guanghui da kuma mai ba da shawara na kungiyar kwararru a fannin fasahar rubutu na kasar Sin Zhang Biao da sauran mutane 100 ko fiye sun halarci bikin bude nunin.(Lami)