Lardin Yunnan ya gudanar da irin wannan aiki, ciki hadda wasan kwaikwayon yaki da miyagun kwayoyi da tinkarar cutur sida, gasar zane-zane cikin makarantu, yin kamfe cikin jirgin kasa ko masana'antu, fadakarwa a tsakanin manoma 'yan kwadago, fadakarwa a wurare dake kan bakin iyakar kasa da dai sauransu.
A lardin Zhejiang kuwa, an kara karfin yin rigakafi kan wannan ciwo. Kuma an yi fadakarwa yadda ya kamata da daukan wasu matakai da suka dace.
Bisa kididdigar da kwamitin kiwon lafiya da kayyade yawan haihuwa na kasar Sin ta gabatar, ya zuwa ran 30 ga watan Satumba, yawan mutane da suka kamu da ciwon sida a raye da wadanda suke dauke da kwayar cutar HIV mai haddasa Sida ya kai kimanin dubu 430. Ban da haka, karin mutane da suka kamu da wannan ciwo daga watan Janairu zuwa watan Satumba na wannan shekara ya kai dubu 70. Jima'i ya kasance muhimmiyar hanya wajen yaduwar cutar ta sida wato AIDS. (Amina)