in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ONUSIDA ta bayyana wani muhimmin ja da bayan kamuwa da cutar kanjamau
2012-11-21 10:33:59 cri

Tsarin hadin gwiwa na MDD kan yaki da cutar kanjamau ONUSIDA ya ba da wani rahoto kan halin da ake ciki game da yaki da wannan cuta a duniya, inda rahoton ya bayyana matakin da aka dauka na gaggauta kawar da wannan annoba. Adadin sabbin mutanen dake dauke da cutar ya ragu fiye da kashi 50 cikin kashi 100 a kasashe 25 dake samun kudin shiga maras karfi ko madaidaici wadanda kuma aka sarinsu suna a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, yankin da wannan cuta ta fi kamari.

Samun saurin cigaban zamani, ya taimaka wajen gudanar da aiki cikin watanni 24 wanda a wani lokacin yake daukar shekaru da dama, in ji mista Michel Sidibe, babban darektan ONUSIDA.

Muna fadada da yawaita ayyukanmu cikin sauri da kuma amfani da ilmi yadda ya kamata. Wannan na nuna cewa, tare da niyyar siyasa da kuma cigaba da aikinmu, ko shakka babu hakarmu za ta cimma ruwa game da tabbatar da maradunmu na hadin gwiwa zuwa nan da shekarar 2015.

A fannin da aka fi samun cigaba sosai shi ne bangaren kananan yara inda aka samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar kanjamau.

Bisa shekaru biyu da suka gabata, rabin kashi na ja da bayan yaduwar cutar sida a duniya an same shi ne a wajen jarirai.

Kuma hakan na nuna cewa, ko shakka babu, akwai yiyuwar cimma muradin kawar da kamuwa da cutar kanjamau daga wajen kananan yara, in ji mista Sidibe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China