Gwamanatin tarayyar Najeriya ta bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa, tana aiki tukuru wajen daidaiye mutuwar dake nasaba da ciwon Sida a cikin yakin da take da wannan annoba.
John Idoko, darekta janar na hukumar yaki da ciwon Sida ta kasa (NACA) ya gabatar a yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja da jawadalin aikin hukumarsa game da ranar kasa da kasa ta yaki da ciwon Sida ta shekarar 2012 mai zuwa.
Duk da matsalar rashin isassun kudade dalilin rikicin kudi na duniya, amma kasar Najeriya ta lashi takobin cimma burin na hana samun sabbin masu dauke da wannan cuta, kawar da bambanci ga mutanen dake dauke da cutar da kuma kawar da mutuwar dake da nasaba da ciwon Sida, in ji wannan jami'i.
Ita dai ranar yaki da ciwon Sida ta duniya, ana gudanar da ita a kowace ranar daya ga watan Disamba, kuma a yayin wannan rana, ana fadakar da mutanen duniya kan illar wannan cuta dake salwantar da rayuka jama'a. A wannan karo, za'a shirya bikin wannan rana bisa taken "sake neman amsa a cikin kasashe wajen cimma burin kawar da mutuwar dake da nasaba da ciwon Sida".
A shekarar da ta gabata, kasar Najeriya ta mai da muhimmanci kan rigakafin yaduwar wannan cuta daga uwa zuwa jinjiri da tare da mai da hankali kan samar da kudade da kayayyaki wajen cimma wannan buri na kawar da mutuwar dake da nasaba da Sida, a cewar mista Idoko.
Daga karshe mista Ikodo, ya nuna cewa, Sida ita kadai ba ta kashewa, ya kamata kuma a mai da hankali kan cututtukan dake da nasaba da Sida, musammun ma ciwon tari da sauransu. (Maman Ada)