in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin na mai da hankali kan rigakafin kamuwa da cutar Sida daga uwa zuwa jinjiri
2013-12-02 10:23:58 cri

Tabbatar da aikin yin rigakafin kamuwa da cutar Sida daga uwa zuwa jinjiri ya kasance wani muhimmin mataki na kiwon lafiyar al'umma ga hukumomin kasar Benin, in ji ministar kiwon lafiya na kasar Benin madam Dorothee Akoko-Kinde Gazard a ranar Lahadi a birnin Porto-Novo na kasar.

Da take magana a yayin bikin ranar kasa da kasa game da yakin cutar Sida karo na 26, Dorothee Gazard ta bayyana cewa, domin amsawa ga wannan muhimmin matakin ganin yadda wannan cuta take kamari a wajen mata da kuma la'akari da yawan kananan yaran da suka kamu da ita, kasar Benin ta aiwatar da wani shirin kasa na gama gari kan yin rigakafin kamuwar wannan cuta tare da nauyin ba da jinya.

An fara aiwatar da wannan shiri a kasar Benin a shekarar 2000 bisa gwajin farko da aka gudanar a cikin asibitocin mata 33 dake birnin Cotonou dake kewaye, a kan yin rigakafin kamuwa da cutar daga uwa zuwa jinjiri, ya kai har zuwa shekarar 2010 a cikin asibitocin mata 415, wuraren addini da na masu zaman kansu na kasar, ayyukan da suka shafi kashi 51 cikin 100, in ji madam Dorothee.

Haka jami'ar ta bayyana cewa, yin rigakafi kamuwa daga uwa zuwa jinjiri wani babban mataki ne dake samar da dunkulallun ayyukan ba da jinya ga ma'aurata wato uwa zuwa jinrinta da mijinta.

Wannan mataki na yin rigakafin ganin yadda aka aiwatar da shi yadda ya kamata ya taimaka sosai wajen rage adadin kamuwa da Sida daga uwa zuwa jinjiri da kashi 35 cikin 100 zuwa kasa da kashi 5 cikin dari.

A kasar Benin, an kara zafafa yaki da cutar Sida a 'yan shekarun baya bayan nan a karkashin jagorancin shugaban kasar Boni Yayi da ya ba da umurnin kebewa gwamnatin kasar Sefa biliyan biyu domin sayen magunguna da kwayoyin rage kaifin cutar a tsawon wannan shekarar 2013. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China