in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta samu gudummawar dala miliyan 300 don yaki da cutar AID
2013-10-09 14:01:47 cri

Asusun yaki da cutukan AIDs ko Sida, da zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka na kasa da kasa, ya baiwa kasar Afirka ta Kudu gudummawar dalar Amurka miliyan 300, domin bunkasa yaki da cutar AIDs mai karya garkuwar jiki.

An bayyana samun wannan tallafi ne yayin taron da cibiyar yaki da cutar ta AIDs ko Sida ta kasar Afirka ta Kudun ta gudanar, a garin Rustenburg dake makwaftaka da birnin Johannesburg.

A cewar mataimakin shugaban kasar, kuma jagoran cibiyar yaki da wannan cuta Kgalema Motlanthe, wannan ne tallafi mafi girma da kasar ta taba samu a wannan fanni na yaki da cutukan AIDs da tarin fuka. Ya kuma yi imanin hakan zai ba da damar habaka yakin da kasar take yi, da wannan cuta mai matukar hadari ga rayuwar al'umma.

Da yake tsokaci kan yadda za a kasafta wannan tallafi, ministan a ma'aikatar lafiyar kasar Aaron Motsoaledi, ya ce, za a mika kaso 52 bisa dari ga ma'aikatar lafiyar kasar, yayin da kuma ragowar kaso 48 zai shiga hannun kungiyoyi masu zaman kansu, da kungiyoyin addinai, da na ci gaban al'umma, da kuma hadaddiyar kungiyar masu dauke da cutar ta kasa.

Mahalarta taron dai na wannan karo sun yaba da irin ci gaban da Afirka ta Kudun ta samu a wannan fanni na dakile yaduwar cutar Sida, wanda ya yi daidai da kudurin MDD, da ya tanaji rage yaduwar cutar da kaso 50 bisa dari nan da shekarar 2015 dake tafe.

Bisa kididdigar baya bayan nan da gwamnatin kasar ta fitar, an ce, kimanin mutane miliyan 2 dake dauke da kwayar cutar ne ke samun magungunan kashe kaifin yaduwarta, matsayin da ya zama mafi nasara a dukkanin fadin duniya.

Kasar Afirka ta Kudu dai na cikin na gaba-gaba, a jerin kasashen Afirka dake da dinbin al'umma dake dauke da wannan cuta ta AIDs, inda cikin jimillar mutane miliyan 22.9 masu dauke da cutar a yankin kudu da hamadar Sahara, mutane miliyan 5.6 'yan kasar ta Afirka ta Kudu ne. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China