in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alkalan Afirka na ganawa game da batutuwan cutar Sida da kare hakkin bil-adam
2013-10-30 10:05:45 cri

Sama da alkalai da majistarori 50 daga nahiyar Afirka ne suka fara wata ganawa ranar Talata, inda za su yi musayar kwarewa game da batun cutar kanjamau dake da nasaba da kare hakkan bil-adan da kuma doka.

Shugaban kotun kolin kasar Kenya mai masaukin bakin, Willy Mutungai, ya ce, taron zai baiwa alkalai da kuma majistororin damar tattauna dabaru da shirye-shiryen da suka dace kan ilimin harkokin shari'a, ta yadda za su taimaka wajen tabbatar da cewa, alkalan sun yanke shawarar da ta dace game da batutuwan da suka shafi cutar kanjamau wadanda ke da nasaba da kare hakkin bil-adam.

Shi dai wannan taro game da cutar kanjamau, kare hakkin, bil-adam da kuma doka, ya hallara jami'an shari'a ne daga kasashen Botswana, Burundi, Kenya, Lesotho, Malawi, Afirka ta Kudu, Swaziland, Tanzaniya, Uganda, da kuma Zambia.

Manufar wannan taron wanda shi ne irinsa na farko a Afirka, ita ce, dorawa kan shawarwarin hukumar yaki da cutar kanjamau a duniya da tsara dokoki wadanda ke da alhakin kara ilimantar da muhimman sassan da abin ya shafa game da batutuwan da suka shafi 'yanci da doka game da cutar Sida tare da karfafawa kungiyoyin fararen hula gwiwar gudanar da kamfel da neman taimako.

Bugu da kari, taron alkalan na nahiyar Afirka, zai samar da wata damar tattaunawa tare da musayar ra'ayoyi tsakanin alkalai da majistarori daga kasar Kenya da wadanda suka zo daga gabashi da kudancin nahiyar game da dokoki masu sarkakiya da batutuwan da suka shafi kare hakkin bil-adam da cutar da kanjamau ta haifar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China