in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 7 na kudu da Sahara sun cimma nasarar rage yawan yara dake kamuwa da cutar Sida
2013-06-26 10:29:22 cri

Wani rahoto na shirin yaki da cutar kanjamau ko Sida na kasa da kasa karkashin hukumar UNAIDS, da hadin gwiwar shirin fadar gwamnatin Amurka na rage yaduwar wannan cuta wato PEPFAR, ya bayyana raguwar yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki, da kaso mai yawa, musamman tsakanin yara kanana a kasashe 7 dake kudu da hamadar Saharar Afirka.

Rahoton wanda aka fitar ranar Talatar da ta gabata, ya tabbatar da cewa, wadannan kasashe sun samu nasarar rage kamuwar yara da wannan cuta da adadin da ya kai kaso 50 bisa dari a bana, idan an danganta da jimillar yaran da suka kamu a shekarar 2009. Wadannan kasashe da rahoton ya lisafta sun hada Botswana, da Habasha, da Ghana, Malawi, da kasar Namibia, da Afirka ta Kudu, da kuma Zambia. Su ma kasashen Tanzania da Zimbabwe, rahoton ya bayyana irin ci gaban da suke samu a wannan fanni.

Shirin yaki da yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki dake da burin rage kamuwar yara kanana da cutar ta Sida, da kuma kare rayuwar iyayensu mata nan da shekarar 2015, wanda aka fara aiwatarwa a shekarar 2011, na da muhimman kudurori guda biyu; wato rage kamuwar yara kanana da wannan cuta da kaso 90 bisa dari, da kuma rage mace-mace sakamakon kamuwa da cutar da kaso 50 bisa dari. Shiri ne kuma da aka tanaje shi, musamman domin kasashe 22 dake kudu da hamadar Saharar Afirka, wadanda ke sahun gaba a yawan yara dake kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki. Rahoton na wannan karo shi ne irinsa na biyu da kasashen yankin 21 suka fitar kan irin ci gaba, da kuma kalubale da suke fuskanta don gane da cimma burin da aka sanya a gaba.

Duk dai da irin wannan gagarumar nasara da wadannan kasashe suka samu, a hannu guda, akwai kasashen da rahoton ya nuna rashin cimma burin da ake fata, irin kasashen da ya zama wajibi a dauki matakin binciko bakin zaren. Har ila yau, rahoton ya bayyana rashin samun isassun magunguna ga yara kanana, a matsayi daya daga manyan kalubale da wannan shiri ke fuskanta, musamman duba da cewa, yara 3 cikin 10 kacal ne ke iya samun magungunan da suke bukata a wadannan kasashe da shirin ya kebe. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China