in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin addini na kasar Sin sun musanta rahoto kan 'yancin addini da Amurka ta bayar
2011-05-06 20:42:35 cri
A ranar 5 ga wata, wasu manyan kungiyoyin addini biyar na kasar Sin sun yi taro a nan birnin Beijing, inda suka musanta rahoto kan 'yancin addini a kasa da kasa a shekarar 2011 da kwamitin kula da 'yancin addini a kasa da kasa na kasar Amurka ya fitar a ranar 28 ga watan Afrilu, kuma a cewarsu, rahoton ba gaskiya ba ne.

Takardar bayan taron da aka fitar ta nuna cewa, ko da yaushe sassan kula da harkokin addini na kasar Sin na mai da hankali a kan 'yancin al'umma na bin addinin da suka ga dama. Sin kasa ce da ke gudanar da harkokinta bisa doka, kuma jama'ar kasar na da cikakken 'yancin bin addini.

Takardar ta jaddada cewa, wasu tsirarun kungiyoyi da mutane sun aikata laifuffuka da sunan addini, wadanda suke lalata tsarin zaman al'umma da hadin kan kabilu, har ma suna kawo barazana ga tsaron kasa, wadanda kuma ba ruwansu da maganar 'yancin addini. Yadda gwamnatin kasar Sin take yakar kungiyoyi addini masu gurbatattun ra'ayoyi da 'yan aware ya zama abin da ya kamata, haka kuma ya dace da burin sassan addini a kasar Sin.

Takardar ta kara da cewa, mambobin kwamitin kula da 'yancin addini a kasa da kasa na kasar Amurka sun taba yin mu'amala da sassan addini na kasar Sin, amma ra'ayoyin da rahoton ya nuna ya saba da yadda suka bayyana a yayin mu'amalar, wannan kuma abu ne mai wuya a fahimta. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China