Yayin ganawa da shugabannin kungiyoyin addinai a birnin Beijing, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Yu Zhengsheng ya ce, manufofin jam'iyyar a fuskar harkokin addini ba za'a sauya su ba.
Manufofin jam'iyyar CPC a fuskar addini sun kunshi mutunta 'yancin addini, gudanar da harkokin addini bisa yadda doka ta tanada, manufar 'yanci da mulkin kai da kuma yiwa addini jagora don ya samu daidaituwa da tsarin gurguzu na kasa.
Yu ya ci gaba da cewa ta hanyar aiwatar da wannan manufa ne kawai za'a iya jan hankulan masu addini da ma wadanda ba su da addini, su shigo aikin hada hannu wajen gina kasar Sin mai wadata a kowace fuska.
Da kuma yake yabawa kungiyoyin addinan dangane da gina kungiyoyin nasu, Yu ya jadadda muhimmancin samun tarbiya ta addini ya kuma yi kira ga kwamitotin CPC da kananan hukumomi da su bada karin goyon baya ga mabiya addinai. (Lami)