Wannan sanarwa ta nuna cewa, bin addini cikin 'yanci wani babban iko ne na mazauna kasar Sin, tsarin mulkin kasar Sin da dokokin da suke da nasaba suna tabbatar da wannan iko kamar yadda ya kamata. A idon gwamnatin kasar Sin, dukkan addinai suna kan matsayin zaman daidai wa daida, babu hulda mai tsanani dake kasancewa a tsakanin addinai daban daban a kasar Amurka.
Bugu da kari, wannan sanarwa ta ce, ba ma kawai wadanda suke son bin addinai suna da 'yanci wajen bin addinai ba a kasar Sin, har ma suna da dukkan halaltaccen iko kamar yadda sauran jama'ar kasar Sin suke da su. Kowane addini na kasar Sin ya nemi mabiyansa da su bi dokokin kasarsu kamar yadda yake a sauran kasashen duniya, ciki har da kasar Amurka. Tabbas ne kasashen duniya, ciki har da kasar Amurka suna shari'ar wadanda suka aikata laifuffuka da sunan.
Game da wannan rahoton da kwamitin bin addinai cikin 'yanci na kasa da kasa na kasar Amurka ya bayar, a ranar Talata 27 ga wannan wata, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, bangaren Sin ya nemi wannan kwamitin Amurka da ya kau da ra'ayoyin nuna bambanci da kuma girmama hakikanin abubuwa na a zo a gani a kokarin kawar da kuskurensa na yin amfani da batutuwa, kamar addini domin tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin. (Sanusi Chen)