Kwanan baya, kwamitin kula da harkokin 'yancin addini na kasa da kasa na Amurka ya ba da rahoto game da 'yancin addini na kasashen duniya na shekarar 2011, inda ya sake yin suka ga kasar Sin. A wannan rana, yayin da Madam Jiang Yu ke zantawa da manema labaru, ta ce, gwamnatin Sin ta tabbatar da 'yancin addini na jama'arta bisa dokokin kasar, kuma jama'ar kasar na da cikakken hakki wajen bin addini cikin 'yanci. Sabo da haka, Sin ta bukaci wannan kwamitin da ya daina nuna bambancin ra'ayi ga kasar Sin, kana ya dakatar da yin shisshigi ga harkokin gida na Sin ta hanyar ba da rahotanni.(Bako)