in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bayyana wasu hanyoyin bunkasa ci gaban Afirka
2013-11-21 10:58:20 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana samar da ayyukan yi, da kuma tallafawa kanana da matsakaitan masana'antu, a matsayin wasu daga muhimman hanyoyin kakkabe talauci, da kuma bunkasa ci gaban nahiyar Afirka.

Ban, wanda ya bayyana hakan cikin sakonsa ga bikin inganta masana'antun nahiyar ta Afirka na shekara shekara, ya kara da cewa, tarin matasa dake cikin al'umma, da kuma ingantacciyar basira, su ne ke haifar da bunkasar masana'antu, don haka Afirka ke da bukatar yin kyakkyawan amfani da hakan wajen habaka ci gabanta.

Babban magatakardar MDDr ya ce, yayin da ake bikin cikar kungiyar tarayyar Afirka ta AU shekaru 50 da kafuwa, kamata ya yi a sa kaimi ga ci gaban nahiyar. Daga nan sai ya ja hankalin kasashe mambobin kungiyar, da su yi aiki tare wajen ganin sun baiwa batun samar da ayyukan yi, da habakar sana'o'i muhimmancin da ya dace.

Taron bunkasa masana'antun nahiyar Afirka, wanda babban zaman MDD na shekarar1989 ya kirkiro, na da nufin zalubo hanyoyin samar da ci gaba ga nahiyar ta wannan fuska. A bana kuma taron ya mai da hankali ne ga tattauna batutuwan da suka shafi samar da ayyukan yi, da kuma yaki da talauci. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China