Kasar Afrika ta Kudu ta yi alkawari a ranar Lahadi na cigaba da gudanar da muhimmin aiki a cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya da tsaro a bangaren shiyyoyi da ma nahiyar Afrika baki daya.
Wannan yana da tushe ga imaninmu na zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a matsayin ginshikan cigaban tattalin arziki da na jama'a, kana wata hanyar dunkulewar kasashen Afrika, in ji ministan harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu a cikin wata sanarwa gabanin taron hadin gwiwa na gamayyar cigaban kasashen kuriyar Afrika da taron kasa da kasa kan yankin Great Lakes.
Wannan dandali zai mai da hankali kan aiwatar da tsarin zaman lafiya, tsaro da kuma hadin gwiwa domin kasar DRC-Congo da shiyyar.
A ranar Talata, Afrika ta Kudu za ta karbi bakuncin wani taron shawarwari kan karfin Afrika wajen warware wasu matsalolin gaggawa (ACIRC). Makasudin wannan haduwa shi ne na tuntubar kasashen da suka bayyana niyyarsu na taimakawa taron da kuma yadda zai yi aiki.
Shugabannin kasashe da na gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar tarayyar Afrika sun dauki niyya a shekarar 2013 ta kafa taron ACIRC na wucin gadi kafin fara aikin gadan gadan na kafuwar rundunar Afrika (FAA) a cikin tsarin yarjejeniyar zaman lafiya da kafa tushen tsaro a Afrika. (Maman Ada)