in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun bukaci amsa guda ta hadin gwiwa kan kalubalen tsaro a Afrika
2013-10-28 10:34:02 cri

Neman bunkasa zaman lafiya a nahiyar Afrika na bukatar amsa guda ta hadin gwiwa da za ta taimakawa cigaban tattalin arziki da na jama'a, in ji wasu kwararru a ranar Lahadi yayin da suke halartar dandalin shawarwarin zaman lafiya na Atlantic karo na uku.

Matsalar rashin tsaro da kwanciyar hankali da wasu kasashen Afrika ke fuskanta, har zuwa yanzu wani kalubale na yunkurin dunkulewar shiyyar Afrika, in ji Victor Borges, shugaban kungiyar cigaba da musanyar ra'ayoyi tsakanin kasa da kasa, a yayin wannan dandali.

Haka shi ma ra'ayin daya ne wajen Saran Daraba Kaba, sakatare janar na kungiyar hadin gwiwar kogin Mano da ke yin kira da a yi kokarin daidaita matsalolin shiyyar da suke janyo rashin tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika.

Dandalin ya samu halartar wakilai 400 da suka fito daga hukumomin gwamnatoci da masu zaman kansu na kasashe kimanin 52 daga Turai, yankin Amurka ta Kudu, Caribbean, Afrika, Amurka, Canada, Sin da kasar Indiya.

A yayin dandali na tsawon kwanaki uku, shawarwarin wannan shekara suka fi mai da hankali kan muhimman batutuwan cigaban shiyyoyi, kalubalen tattalin arziki, muhalli da makamashi a yankin Atlantic, tasowar kasashe kamar Brazil, matsayin kasar Sin da kuma tasowar Afrika da Latin Amurka a dandalin duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China