Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana aniyar kasarsa, don gane da ci gaba da marawa ofishin UNOCA na MDD baya, a kokarin da yake yi na wanzar da yanayin zaman lafiya da daidaito a kasashen tsakiyar Afirka.
Liu, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba 20 ga watan nan, yayin bude taron nazarin ayyukan ofishin na UNOCA, da batutuwan da suka shafi kungiyar 'yan tawaye ta LRA dake Uganda.
Cikin jawabin da ya gabatar, Liu, ya bayyana matukar bukatar da ake da ita, ta hawa teburin tattaunawa, domin kawo karshen irin tarin kalubalen karancin tsaro, da kwanciyar hankali dake addabar tsakiyar Afirka, musamman ma a kasar Afirka ta Tsakiya CAR wadda ke fama da tashe-tashen hankali. Don gane da halin da ake ciki a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo kuwa, Liu ya bayyana farin cikinsa ga irin ci gaban da ake samu, yana mai cewa, Sin na goyon bayan kasar, da ma ragowar kasashen dake yankin manyan tafkunan Afirka, a fagen hadin gwiwa, da yaki da laifukan da suka shafi fashin teku, da ta'addanci, karkashin tallafin ofishin shiyyar na MDD. (Saminu)