Sakamakon wani binciken da wasu masanan kasar Sin suka gudanar ya nuna cewa, da yawa daga kamfanoni, da cibiyoyin cinikayya masu zaman kansu na kasar Sin dake nahiyar Afirka na gudanar da ayyukan tallafawa al'umma sama da takwarorin su na yammacin duniya dake nahiyar.
Binciken wanda Farfesa Liu Qinghai da wasu malamai a cibiyar nazarin harkokin da suka jibanci Afirka dake jami'ar Zhejiang suka gudanar, ya nazarci wannan batu ne ta hanyar tuntubar wasu mutane 100, daga kasashen Najeriya da Senegal tsakanin watan Nuwamban shekarar 2011 zuwa watan Yulin shekarar bara. Inda sakamakon ya nuna cewa, kamfanoni da cibiyoyin kasar Sin dake Afirka, sun taka rawar gani wajen daukar ma'aikata 'yan asalin nahiyar ta Afirka, tare da samar musu da kyakkyawan yanayin aiki.
Da take gabatar da sakamakon binciken ga mahalarta taron karawa juna sani na hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afirka a ranar Laraba 23 ga wata, Liu ta ce, duk da albashin da kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin ke biya bai kai ga matsayin koli ba, a hannu guda albashi ne da za a sanya a madaidaicin matsayi, wanda kuma ya dace da dokokin kasashen da kamfanonin ke gudanar da ayyukan nasu. (Saminu)