in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron hadin gwiwar kasashen Larabawa da Afirka karo na uku
2013-11-21 10:27:10 cri

An kammala babban taron hadin gwiwar kasashen Larabawa da na nahiyar Afirka karo na uku a kasar Kuwait, tare da cimma yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin yankunan biyu, wadda ta shafi muhimman fannonin ci gabansu.

Taron wanda ya gudana a jiya Laraba 20 ga wata, ya samu halartar shuwagabannin sassan biyu kimanin 70, wadanda suka amince da yin hadin gwiwa wajen yaki da ayyukan ta'addanci, da fasa kwauri, tare da burin bunkasa hadin kai daga dukkanin fannoni.

Karkashin yarjejeniyar ta Kuwait, sassn biyu sun bayyana aniyarsu, ta daukar matakan zakulo, tare da dakile dalilan da suke haifar da rikice-rikice a wadannan yankuna. Har ila yau yarjejeniyar ta tanaji lalubo hanyoyin inganta rayuwa, da zamantakewar al'ummun dake sassan biyu.

A jawabinsa na rufe taron, sarkin kasar ta Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-sabah, cewa ya yi, kasashen Larabawa da na Afirka, na fuskantar namijin aikin warware matsalolinsu, don haka kamata ya yi a zage damtse wajen aiki tukuri, tare da bibiyar ci gaba da ake samu, da ma kalubalen da ka iya biyo baya.

Bugu da kari jagororin bangarorin biyu sun alkawarta ci gaba da gudanar da irin wannan taro bayan dukkanin shekaru uku uku, tare da alkawarta gudanar da taron na gaba a Afirka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China