in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai kyakkyawan fatan bunkasar tattalin arzikin Afirka, in ji babban bankin Afirka ta Kudu
2013-11-12 10:32:42 cri

Mataimakin gwamnan babban bankin kasar Afirka ta Kudu Daniel Mminele, ya ce, akwai alamu dake nuna irin ci gaba, da tattalin arzikin kasashen dake nahiyar Afirka za su samu, duk kuwa da irin kalubalen da ake fuskanta.

Mminele wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin 11 ga wata, yayin taron karawa juna sani kan harkokin cinikayya da aka gudanar a birnin Johannesburg, ya kara da cewa, Afirka na habaka sannu a hankali a fannonin tattalin arziki, sakamakon ingantar tsarin shugabanci a mafi yawan kasashen dake nahiyar.

Har ila yau mataimakin gwamnan bankin na Afirka ta Kudu, ya ce, karuwar mutane dake matsakaicin matsayin tattalin arziki, na cikin dalilan da ke bunkasa ma'aunin GDPn kasashen dake nahiyar.

Bugu da kari Mminele, ya bayyana cewa, kalubalen da kasuwannin kasashen da suka ci gaba suka fuskanta, sakamakon matsalolin tattalin arziki da ta mamaye duniya, ta zo daidai gabar da kasashe masu tasowa ke samun bunkasuwa, matakin da ya ba da damar bunkasar hada-hadar fidda kayayyaki zuwa ketare, wanda hakan ya dada karfafa kasuwannin fidda kayayyakin dake nahiyar ta Afirka.

A baya ma dai bankin raya Afirka na ADB, ya bayyana cewa, kudaden da al'umma dake matsakaicin matsayin tattalin arziki ke kashewa sun kai dala miliyan dubu 680, kimanin kaso 25 bisa dari na ma'aunin GDPn nahiyar a shekarar 2008 da ta gabata.

An kuma ce, wannan adadi na iya kaiwa dala tiriliyan 2.2 nan da shekarar 2030, matakin da bankin na ADB ke ganin tabbas zai dada karfafa tattalin arzikin nahiyar ta Afirka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China