Nahiyar Afrika na samar da wasu sharudan zaman rayuwa masu kyau ga kananan yara bisa ga shekaru biyar da suka gabata, a cewar dandalin manufar kasashen Afrika game da yara ACPF.
Rahoton na bayyana sakamakon bincike kan zaman rayuwar kananan yara da aka gudanar a kasashen Afrika 52.
Wannan rahoto ya fito a ranar Talata a birnin Addis Ababa na kasar Habasha mai taken 'rahoton Afrika kan kyautatuwar rayuwar kananan yara na shekarar 2013 dake mai da hankali kan nauyin dake kan wuyan gwamnatocin kasashen Afrika game da yaran Afrika', tare kuma da bayyana imanin cewa, kyautatuwar rayuwar kananan yara na dogaro da tattalin arzikin kasashen Afrika.
Kasashen nahiyar Afrika dake nuna mihimmanci sosai ga yara sun hada da Maurice, Afrika ta Kudu, Tunisia, Masar, Cap-Vert, Rwanda, Lesotho, Aljeriya, Swaziland da Marocco, a cewar wani rahoton bincike da ke nazari da ba da maki kan cigaban kasashe daban daban ta hanyar gabatar da alkaluma na kiwon lafiyar kananan yara tare da kwatanta su da sauye-sauyen da aka samu tun bayan binciken da aka gudanar a shekarar 2008.
Bunkasuwar tattalin arzikin da ake gani baya bayan nan a nahiyar Afrika za ta kasance wani mataki na zahiri wajen rage talauci da bambance-bambance da kuma kara samun kason kudi da za'a a shigar da shi ga kyautatuwar rayuwar kananan yara a Afrika, in ji mista Theophane Nikyema, darektan zartarwa na ACPF. (Maman Ada)