Yau Laraba 20 ga wata, an yi tattaunawa tsakanin kasashe biyu na kasashen da abin ya shafa, sai a ranar 21 ga wata, za a gudanar da cikakken zaman taro na kasashen nan shida batun nukiliyar kasar Iran ya shafa da kasar Iran.
Bisa labarin da aka samu, yau da yamma bisa agogon wuri, babbar wakiliyar EU mai kula da harkokin dipliomasiya da tsaro kungiyar EU Catherine Ashton za ta yi shawarwari tare da ministan harkokin waje, babban wakili mai kula da shawarwarin batun nukiliyar kasar ta Iran Mohammad Javad Zarif. Bugu da kari, tawagar kasar Sin dake karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Li Baodong ta riga ta isa birnin Geneva, kuma yau da yamma, Mr. Li Baodong zai gana da wakilan kasashen Amurka da Rasha. (Maryam)