in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Iran za ta kula da harkokin yin shawarwari tare da kasashe shida kan batun nukiliya na kasar
2013-09-06 14:53:32 cri
Ran 5 ga wata, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya sanar da cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar za ta kula da harkokin yin shawarwari na karo mai zuwa a tsakaninta da kasashe shida wato Amurka, Ingila, Faransa, Rasha, Sin da Jamus kan batun nukiliya na kasar.

Bisa labarin da aka samu a wannan rana daga kamfanin dillancin labaran kasar Iran, an ce, kudurin nan da shugaban kasa ya tsayar, ya nuna cewa, a maimakon babban kwamitin tsaron kasar, ma'aikatar harkokin wajen kasar ce za ta shiga shirin yin shawarwari game da batun nukiliyar kasar tare da kasashen shida. Amma shugaba Rouhani bai nuna cewa ko zai nada ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif a matsayin shugaban tawagar shawarwari ta kasar Iran ko a'a ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China