Babban mai shiga tsakani game da batun nukiliyar kasar ta Iran Saeed Jalili da kuma bangarori shida da batun ya shafa, ya ce wasu daga cikin batutuwan da aka gabatar suna bisa turba, idan aka kwatanta da abin da suka gabatar a baya.
Bangarorin shida wadanda suka hada da Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da kuma Jamus, sun yi tayin janye wasu takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran ta yadda za a daidaita game da shirinta na nukuliya da ake takaddama a kai.
Jalili ya ce, suna kokarin samar da wani tudun dafawa kan wasu batutuwa da Iran din ta gabatar da kuma nasu bangaren, matakin da ya yi imanin cewa wani babban ci gaba ne, duk da cewa akwai sauran rina a kaba game da matsayin da ake son cimmawa.
Bangarorin biyu sun amince su suke ganawa game da shirin nukiliyar kasar ta Iran da bangarori shida da batun ya shafa a watan Afrilu bayan kwararru kan nukiliya sun gana a Istambul na kasar Turkiya a watan Maris. (Ibrahim)