Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban kasar Faransa Francois Hollande da ya kai ziyara a kasar a yammacin ranar Lahadin nan, inda ya mika godiyarsa a kan matsayin da Faransa ta dauka game da batun nukuliyar kasar Iran.
Netanyahu dai tare da Hollande sun gana da manema labarai tare bayan tattaunawarsu a ofishin firaministan a birnin Jerusalem, inda suka jaddada muhimmancin dangantaka a tsakanin kasashensu da kuma hadin gwiwwa da ya shafi tattaunawar kasashe 6 tare da kasar Iran da za'a yi a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Mr. Netanyahu ya ce, Isra'ila na goyon bayan zaman lafiya da huldar diplomasiyya a matsayin hanyar da za'a iya bi wajen sulhunta halin da ake ciki a yanzu, sai dai ya nuna rashin jin dadinsa game da matsayin da aka dauka na kyale kasar Iran ta cigaba da samar da sinadarin uranium, yana mai cewa, hakan ya ba Iran wata dama, inda ta nuna jin dadinta a bayyane wanda hakan wani mummunan sakamakon da zai haifar wa duniya baki daya.
Shugaban kasar Faransa a nasa bangaren ya nuna fahimtar korafin firaministan Isra'ila game da hakan, inda ya ce, bukatarsu ita ce Iran ta dakatar da kera makaman nukiliya. Duk da dai cewar, akwai cigaba a cikin tattaunawa da kasar ta Iran, amma wannan bai wadatar ba, in ji shi, yana mai nuni da taron Geneva da za'a yi.
A don haka sai ya ce, suna sa ido su sami wani abin da zai ba su tabbacin hakan, kuma a lokacin taron Geneva, za su matsa lamba a kan Iran. (Fatimah)