A wannan rana ne kuma, aka kira taron kwamitin sulhu na MDD, inda aka saurari rahoton da kwamitin yanke hukunci ga kasar Iran ya gabatar. Yayin taron, Wang Min ya ba da jawabi cewa, ya kamata bangarorin daban daban da abin ya shafa su dauki alhakin aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD yadda ya kamata, amma ainihin burin kudurin ba yin hukunci kan kasar Iran ba ne. A kullum kasar Sin na ganin cewa, ya kamata kwamitin yanke hukunci da kungiyar masana su ba da taimako wajen aiwatar da shawarwarin da ke tsakanin bangarorin da abin ya shafa bisa fahimta da kuma amincewar juna, ta yadda za a iya warware matsaloli ta hanyar diplomasiya. Kuma kamar yadda kasar Sin ta nuna a kullum cewa, ba ta amince da hanyoyin kawo wa kasar Iran barazana ko ci gaba da daukar sabon takunkumi kan kasar ba.
Wang Min ya kuma kara da cewa, kasar Sin na goyon bayan kasar Iran wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da hukumar makamashin nukiliyar kasa da kasa, don samar da sakamako mai gamsarwa cikin sabon shawarwarin da za a yi ran 27 ga watan Satumba. (Maryam)