in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya bukaci senatocin Amurka da su dan jinkirtar da sabbin takunkumi kan Iran
2013-11-20 10:50:59 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi kira ga senatocin kasarsa da su dan jinkirtar da jefa kuri'a game da sabbin takunkumin tilastawa kan kasar Iran, domin taimakawa kokarin da mambobin gwamnatinsa suke na cimma wata yarjejeniya kan shirin nukilkiya na Iran da ake takadama kansa tare da hukumomin Teheran.

Shugaba Obama tare da kwamitinsa na tsaron kasa dake kunshe da sakataren harkokin kasa John Kerry da mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa Susan Rice sun gudanar da kebabben taron sirri na awowi biyu a fadar 'White House' tare da shugabannin majalisar senatocin kasar da kuma manyan jami'an kwamitin banki, da na hulda da kasashen waje, manyan jami'an rundunonin sojojin kasar da kuma na leken asiri.

Shugaban Amurka ya jaddada cewa, cimma wata mafita ta hanyar sulhu zai hana Iran tanadar makaman nukiliya tare kuma da samun dabara mafi alfanu ga tsaron kasar Amurka, in ji kakakin fadar shugaban kasar Amurka mista Jay Carney a yayin wani taron menama labarai.

Haka kuma jami'in ya bayyana cewa, bai kamata ba a fara sabbin takunkumi ba domin ana cigaba da yin shawarwari, amma za su kasance wani makami mai kyau ga wani yunkurin kaurace wa tayin gungun P5+1 da suka hada da Sin, Amurka, Faransa, Burtaniya, Rasha da kuma Jamus daga bangaren Iran, ko kuma idan har kasar Iran ba ta girmama alkawuran da ta dauka ba, in ji mista Carney. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China