in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa sun ba da sanarwa cikin hadin gwiwa a karo na farko
2013-10-17 11:52:06 cri
Ran Laraba 16 ga wata, aka kammala taron shawarwari tsakanin kasashe shida da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa da kasar ta Iran a birin Geneva dake kasar Switzerland, inda suka ba da wata sanarwa cikin hadin gwiwa a karo na farko, da kuma sanar da cewa, za a ci gaba da taron shawarwari tsakanin kasashen shida da kasar Iran na wani sabon zagaye a birnin Geneva daga ranar 7 zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba.

Yayin taron manema labaran da aka yi bayan taron shawarwarin, babban wakiliyar kungiyar tarayyar kasashen Turai mai kula da harkokin difomasiyya da tsaro na Catherine Ashton ta bayyana cewa, bangarorin daban daban da abin ya shafa sun riga sun cimma ra'ayi daya, amma a halin yanzu, ba za a sanar da karin bayani kan taron shawarwari da kuma abubuwan da aka tattauna a taron ba.

Ranar Laraba, kakakin fadar White Hhose ta kasar Amurka Jay Carney ya bayyana cewa, yayin taron shawarwarin da aka yi a wannan mako, kasar Iran ta nuna hadin gwiwa sosai kan shawarwarin da aka fitar wajen warware batun nukiliyarta. Amma, Mr. Carney ya jaddada cewa, ya kamata kasar Iran ta cika alkawarin da ta yi wa gamayyar kasa da kasa, bugu da kari, kamata ya yi, dukkan yarjejeniyoyin da aka sa hannu kan batun nukiliyar kasar Iran za su kasance na buri guda ne kadai, watau na zaman lafiya.

A wannan rana kuma, babban sakataren kula da harkokin kasashen wajen kasar Burtaniya ya bayyana cewa, kasar tana fatan za a iya samun sakamako mai gamsuwa kan batun nukiliyar kasar Itan cikin sauri.

Shugaban tawagar wakilan kasar Sin, kuma shugaban sashen kula da harkokin kwance damara na ma'aikatar harkokin wajen Sin Pang Sen ya bayyana a birnin Geneva cewa, kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su gane darajarta damar da aka samu, da kuma yin amfani da ita wajen ciyar da aikin warware batun nukiliyar kasar Iran gaba. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako yadda ya kamata don warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar siyasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China