Mr. Lavrov ya kuma yi watsi da zargin da ake cewa, wai kasar Iran din tana jan lokaci ne kawai don ta samu damar samar da bam din nukiliya, abin da ya bayyana cewa, wannan magana ce ba ta kamawa ba.
Tun da farko dai kasar Iran ta ce, a shirye take ta amince da duk shawarar da kasashen da abin ya shafa suka tsai da, in dai shawara ce nagartacciya .
Kasar Iran da sauran manyan kasashen da abin ya shafa wato Birtaniya, Amurka, Sin, Rasha, Faransa da Jamus wato kungiyar P5+1 za su dawo da tattaunawa a kan batun nukiliyar kasar Iran a Geneva a Laraban nan 20 ga wata bayan kammala tattaunawar da aka fara a makon da ya gabata ba tare da cimma matsaya ba.(Fatimah)